<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>87</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Ku masu Ƙaunar Yesu fa, jama'ar Masu Bi,
 Ku kasance da halin da ya zauna cikinsa.

[V2]
 2) Ko cikin surar Allah, shi, girmansu ɗaya ne,
 Ya ƙanƙantad da kansa, har ya zama bawa, shi

[V3]
 3) Ya zama gurbinmu a nan, ya yi biyayya, shi,
 Biyayya har ga mutuwa, mutuwar giciye.

[V4]
 4) I, domin wannan Allah kuwa ya ƙara girmansa,
 Ya ba shi suna mafi kyau a bisa kowanne.

[V5]
 5) I, domin girman sunan nan, sunansa mafi kyau,
 Gwiwoyin dukan masu rai duk za su rusuna.

[V6]
 6) Kowane harshe cikinsu zai yi shaidar Yesu,
 Cewa shi Ubangiji ne don girman Allahnmu.</lyrics>
<title>Ku Masu Ƙaunar Yesu Fa, Jama'ar Masu Bi LW87</title>
</song>